Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Ms. Audrey Azoulay, ta ce a shekarar 2023, kashi 60% na al’ummar duniya mai jimillar mutane biliyan 4.75, sun rungumi amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana abubuwan da suka shafe su da neman amsoshin tambayoyi da sauran mu’amala.
Ms. Audrey, wanda Darakta na Hukumar UNESCO ta Nijeriya, Mista Diallo Abdourahamane, ya wakilta, ta bayyana hakan a yayin bikin Ranar Amfani da Kafofin Yada Labarai da Yada Bayanai ta bana, ranar Laraba, a Abuja.
Ta yi bayani a kan alfanun hanyoyin sadarwa na zamani da kuma kalubalen da suke haifarwa ga al’umma.
A cewarta, “Ana sa ran UNESCO nan ba da jimawa ba za ta fitar da dabarun daidaita tsarin dandamali na fasahar sadarwa, da samar da umarni na bai-daya da za a rika amfani da shi wajen auna kididdiga, yadda ake aiki da harkoki daban-daban, da tabbatar da ingancin tattara bayanai da adana su, da kiyaye sirri da kuma tabbatar da ‘yancin dan adam.”
“UNESCO, ta himmatu wajen inganta tunani mai mahimmanci da kuma kauce wa amfani da tsattsauran ra’ayi mara misali a tsakanin jama’a da yawa,” in ji ta.
A nashi jawabin, Ministan yada labarai, Mohammed Malagi, wanda Misis Comfort Ajiboye ta wakilta ya ce, “a yau, muna rayuwa a wani zamani da ake tafiyar da komai cikin sauri ta hanyar fasahar zamani, shi ya sa musayar bayanai ke gudana ba tare da wahala ba.
“Amfanin hakan ga duniya, abu ne mai girma wanda ba za a iya musantawa ba kuma wanda ya ba mu damar yin hulɗa tare da mutane a duk Nahiyoyi, da kuma samun damar koyon ilimi mai yawa, da kawo canji mai kyau a cikin al’ummarmu.
“Ilimi game da harkar yada labarai ya kasance babban jagora ga ci gaban ƙasa wajen amfani da damammaki marasa iyaka waɗanda intanet da sauran kafofin fasahar sadarwa na zamani suke bayarwa”.
Har ila yau, a yayin taron dai, an yi wata tattaunawa da mahalarta game da yadda za a iya amfani da ilimin amfani da kafofin watsa labarai don kawo babban ci gaba a cikin al’umma da kuma yadda za a iya magance rashin fahimta.