Wani kudiri da aka amince da shi jiya Litinin, ya bayyana cewa hukumar kula da ilimi, kimiyya da al’adu ta MDD (UNESCO) na shirin kafa wata cibiya mai daraja ta 1 a fannin kimiyya, fasaha, injiniya da kuma lissafi (STEM) a birnin Shanghai na kasar Sin.
Taron hukumar gudanarwar UNESCO karo na 216 ya bayyana cewa, kafa irin wannan cibiya zai karfafa jagororin kungiyar a fannin ilimin kimiyya, fasaha, injiniya da kuma lissafi. Bugu da kari, za ta ba da gudummawa ga aiwatar da manufofin UNESCO da kuma ajandar ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030.
Cibiyoyin UNESCO masu daraja ta 1, suna kara karfin kimiyya a cikin kasashe mambobin hukumar.
Kudirin da aka amince da shi na kafa cibiyar a kasar Sin, har yanzu yana bukatar amincewar babban taron UNESCO karo na 42 da ke tafe a watan Nuwamba. Kuma da zarar an amince da shi, za ta zama cibiyar hukumar ta farko a kasar Sin da ma wajen Turai. (Ibrahim)