Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Sun Weidong, ya kirawo jakadan Japan dake kasar a jiya Lahadi, don bayyana rashin dadin kasarsa game da gishirin da mahalarta taron kolin G7 suka kara kan batutuwan dake da nasaba da kasar Sin.
Mista Sun ya ce, mambobin G7 sun nace ga tunanin yakin caccar baka, matakin da ya sabawa halin da ake ciki da da’ar kasa da kasa. Ya ce a matsayin kasar dake da shugabancin karba-karba na G7, Japan ta hada hannu da sauran kasashe masu ruwa da tsaki don shafawa kasar Sin bakin fenti da tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida, abin da ya sabawa ka’idojin kasa da kasa da ruhin takardu guda 4 da kasashen Sin da Japan suka sa hannu a kai, da keta ikon mulki da tsaro da muradun kasar Sin, a don haka Sin ke bayyana matukar rashin jin dadinta kan hakan.
Ban da wannan kuma, Mista Sun ya jadadda cewa, a matsayin babbar kasar dake kokarin sauke nauyin dake wuyanta, Sin tana nacewa ga kiyaye tsarin duniya karkashin MDD, da kuma zaman oda da dokar kasa da kasa bisa tushen dokokin da ma ka’idojin huldar kasa da kasa karkashin ka’idojin MDD, kuma ba za ta yarda wasu kasashe su kirkiro ka’idoji bisa radin kansu ba. A cewarsa, wasu kasashen yamma suna tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe da sarrafa harkokin duniya yadda suka ga dama, amma sam ba za su cimma nasara ba. Ya ce Sin na kalubalantar mambobin G7 da su bi hanyar da ta dace da halin da ake ciki, su daina mayar da wani saniyar ware bisa bukatunsu, su kuma dakatar da matsawa sauran kasashe lamba da kawo baraka da yin takara.
Sun Weidong ya ce dole ne Japan ta daidaita ra’ayi da tunaninta don nacewa ga takardu 4 da Sin da Japan suka rattaba hannu a kai, ta yadda za a raya huldar dake tsakanin kasashen 2 yadda ya kamata. (Amina Xu)