Da safiyar yau Alhamis ne, uwargidan shugaban kasar Sin, Peng Liyuan, ta tattauna tare da uwargidan shugaban kasar Kenya, madam Rachel Ruto, wadda ta raka mai gidanta ziyarar aikin da yake yi a kasar Sin a halin yanzu.
A wajen tattaunawarsu, madam Peng ta bayyana nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin yaki da talauci, tare da jinjina wa Rachel saboda kokarin da ta dade tana yi a fannin tabbatar da walwalar al’umma, da mayar da hankali kan baiwa mata ilimi tare da tabbatar da hakkinsu. Peng ta kuma yi fatan bangarorin biyu za su yi musayar dabarunsu, don ciyar da harkokin yaki da talauci da na mata da yara na kasashen biyu gaba.
A nata bangaren, madam Rachel ta yi babban yabo ga madam Peng Liyuan, ganin yadda take kokarin bayar da gudummawa cikin dogon lokaci ga daukaka ci gaban harkokin mata da yara a kasashen Afirka, ciki har da Kenya, kana, ta yi fatan ci gaba da bayar da gudummawarta a fannin inganta mu’amala tsakanin jama’ar kasashen biyu, da yaukaka zumunci a tsakaninsu. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp