Vinicius Jr Mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Dake Spain zai Sanya riga Mai lamba 7 a kaka mai zuwa bayan barin kungiyar da Eden Hazard yayi a kakar bana
Vinicius Jr Wanda yake Sanya riga mai lamba 20 zai zama dan wasa na uku da zai saka rigar tun Bayan tashin Cristiano Ronaldo a Shekarar 2017
Haka ma matashin dan wasa Rodrygo shima zaa canza masa lamba daga 21 zuwa 11 bayan barin kungiyar da Marco Asensio yayi a Karshen kakar bana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp