An harbe wani mutum har lahira da garkuwa da wasu mutum hudu ciki har da Sarakunan gargajiya biyu ne aka yi garkuwa da su a kauyen Balma da unguwar Kutumbawa a karamar hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.
Ana tunanin wadanda suka kai farmakin masu garkuwa da mutane da neman kudin fansa.
- ‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa 2 Da Ceto Mutum 1 A Bauchi
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 4 Da Garkuwa Da 1 A Bauchi
Hare-haren biyu sun faru ne a wurare daban-daban kuma dukka hare-haren sun faru ne da safiyar ranar Lahadi.
Wani da abun ya faru kan idonsa a kauyen Balma, ya shaida cewar lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi inda ya ce masu garkuwan sun shiga kauyen ne a daren ranar Asabar da misalin karfe 11, inda suka gudanar da aika-aikar ta su.
Ya ce kai tsaye ‘yan bindigar suka nufi gidan Sarkin garin tare da bude wuta yayin da jama’a kuma suka ranta a na kare domin neman tsira.
“Bayan da suka yi garkuwa da Sarkin, sun tafi sun bar wani Alhaji Haruna a kwance bayan da suka harbe shi, an garzaya da shi asibitin Ningi sai dai Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa.” Cewarsa.
Majiyar ta kara da cewa ‘yan bindigar daga bisani sun mamaye gidan wani mutum a Bakutunbe inda suka yi garkuwa da Idris Mai Unguwa da wani Ya’u Gandu Maliya, inda tunin suka nemi naira miliyan 8 ga kowannensu a matsayin kudin fansa.
Wannan lamarin na zuwa ne kasa da mako guda da garkuwa da wasu Fulani masu a kauyen Yelwa dukka a karamar hukumar ta Ningi.
Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Bauchi, Sufuritendan Ahmed Muhammad Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin.