‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da Dr. Adekunle Raif Adeniji, daraktan gudanarwa a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a Abuja, sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 350.
Rahotanni sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalansa, inda suka jaddada cewa, sai an biya su adadin kudaden da suka bukata kafin ya shaki iskar ‘yanci.
- Gwamnati Na ɗaukar Matakai Don Rage Farashin Abinci Ta Hanyar Zuba Jari A Noma – Minista
- ’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
Wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 sun yi garkuwa da Dr. Adeniji ne makonni biyu da suka gabata a unguwar Chikakore da ke Kubwa, a cikin karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja.
An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin.
An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin.
Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa mai suna, Madam Esther, a kusa da unguwar Ijah-Gbagyi da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja da safe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp