Kungiyar tuntuba ta Katsina ta shirya wani taron masana da masu ruwa da tsaki akan batun sha da fatauchin miyagun kwayoyi a Jihar Katsina wanda shi ne irin sa ne na farko da sabuwar kungiyar ta shirya.
Shugaban kungiya Alhaji Aminu Abubakar Danmusa ya bayyana cewa taron zai rika daukar matsalolin da ake fuskanta daya bayan dayan yana tattaunawa tare da lalubo hanyoyin da za a tunkare su domin magancewa.
- Ya Kashe Limami Saboda Ya Hana Su Shan Wiwi A Kusa Da Masallaci A Kano
- Shekarar 2024: Kyautata Fata A Cikin Duniyar Kalubale
Taron wanda aka gudunar da shi a ranar lahadin da ta gabata a fadar gwamnatin Jihar Katsina a iya cewa ya bar baya da kura, domin wasu sun fara dora alamar tambaya a kan taron tun kafin gudanar da shi, inda suke cewa me zai kai taron kungiyar da ba ta gwamnati ba a cikin gidan gwamnati maimakon wani wuri daban illa dai kawai a gayyaci bangaran gwamnati saboda irin rawar da zai iya takawa.
Wasu kuma na ganin taro irin wannan bai cika samun makaoma mai kyau ba domin an sha yin irin sa ba tare da ganin wani sakamakon mai kyau ba.
Kamar yadda aka tsara masana sun gabatar da kasidu da suke da alaka ta kai-tsaye a kan wannan matsala ta sha da fataucin miyagun kwayoyi a Jihar Katsina da kuma arewacin Nijeriya baki daya. Haka kuma sun bayyana abubuwa guda hudu da suka ce bincike ne ya nuna su a wannan matsayi.
Abubuwan da masana suka zayyana sun hada da cewa Jihar Katsina ita ce ta biyu wajan sha da fataucin miyagun kwayoyi sannnan mata da matasa (mata masu juna biyu) su ne suka fi sha da ta’amuli da kuma yadda al’umma ta koma ba mai tsawata mata, daga karshe masana suka ce dole sai an cire gwamnati daga wannan yaki idan ana son cimma nasara.
Akwai manyan mutane guda hudu da suka gabatar da kasidu a wajan wannan taro da suka hada da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ce idan ana son cimma nasarar wannan yaki dole sai an hada kai da gwamnatoci kafin a fuskancin wannan matsala gadan-gadan.
Shi ma baban kwamadan mai kula da shiyyar Kano na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Alhaji Sule Mamandu ya yi kira da babbar murya wajan neman taimako daga gwamnatoci musamman na jihohi domin samun dama da kwarin gwiwar yin aikin ka-in-da-na-in a kan wannan matsala.
Shi ma masani a kan harkokin harhada magunguna da siyasa Dakta Usman Bugaje ya yi bayanin cewa sha da ta’amuli da kwayoyi su ne jagaba wajan samuwar yawaitar fashi da makami da aikin ‘yan bindiga da masu yi wa yara fyade saboda haka ya ja hankali gwamnati da sauran al’umma da cewa a tashi tsaye a kan wannan batu kafin ya gama kai wani matsayi na la haula.
Mutane irin su Dakta Muhkhat El-Kasim Malami a tsangayar koyan aikin Jarida a jami’ar Amadu Bello da ke Zariya kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum yana ganin irin wannan taro da wannan kungiya ta “KCF” ta shirya an wuce shi tuntuni, inda ya ce abinda suke sa ran gani shine duk matsalolin Nijeriya an riga an san su, abin da kawai ya rage shi ne daukar matakai wanda za su nuna da gaske ake yi wajan magancewa.
“Abin da na zata shi ne, wannan kungiya za ta zo da wasu tsare-tsare na daukar mataki a kan matsalar sha da ta’amuli da miyagun kwayoyi ba zaman tattaunawa ba wanda daman an saba yin sa, sannan a wajan wannan taro babu wani abu da aka rubuta wanda da ke nuna za a dauki mataki na gaba, sai dai daman ana fitowa da bayanin bayan taro wanda su KCF ba su yi haka ba balanta a ga abin da suka tsara” in ji shi.
Ya kara da cewa shi a nashi ra’ayin, zai so ya ga cewa bayan gama wannan taro mataki ne kawai aka dauka ba tare da bata lokaci ba, ya cigaba da cewa an yi irin wnanan taron a karkashin gwamnatin Aminu Bello Masari da ta gabata inda aka dauki kwana uku ana taro da zummar daukar mataki kan irin wannan matsala amma dai shiru.
Ita kuwa shugabar gidauniyar Kueen Dijah, wanda tana daga cikin wadanda aka gayyata kuma aka ba su damar yin ta’aliki a wajan wannan taro, Hajiya Hadiza Saulawa ta kalubalanci wannan taro da cewa ba ta amince da wasu abubuwa guda biyu da aka zayyana ba wanda ta ce babu alkalumma na hakika game da abin da masana suka bayyana guda hudu.
“Gaskiyar magana ban amince da cewa Jihar Katsina ita ce ta biyu ba wajan sha da ta’amuli da miyagun kwayoyi ba a Nijeriya, ina aka bar jihohin kudu, kuma ban amince da cewa wai sai an cire gwamnati sannan za a iya maganin wannan matsala ba, bayan cewa ‘yan siyasa da suke rike da madafun iko, su ke jefa matasa a wannan harka, dole sai gwamnati da al’umma sun hada karfi da karfe wajan tunkarar wannan matsala idan ana so a samu nasara” Inji Saulawa
Sai dai kuma ta bayyana cewa idan har wannan kungiya ta ‘KCF’da gaske ta yi to ta tabbatarwa da gwamnatoci cewa dole su shiga cikin wannan yaki sannan su amince suna da sa hannu wajan lalacewar al’umma kafin a samu nasara wannan aiki.
A nata banagaren gwamnatin Jihar Katsina ta bakin mataimakin gwamna Malam Faruk Lawal Jobe ya bayyana irin kokarin da gwamnatinsu ta yi wajan tunkarar wannan matsala inda ya ce har motocin sunturi sun raba wa sauran jami’an tsaro da za su taimaka wajan kai farmaki ga masu sha da ta’amuli da miyagun kwayoyi.
Malam Faruk Lawal Jobe yana mai cewa gwamnatinsu a shirye take wajan ganin ta bada duk irin gudunmwar da ake bukata wajan kawo karshen wannan matsala da ta zame wa Jihar Katsina da arewacin Nijeriya karfen kafa mai wuyar datsewa.
Ya zuwa yanzu dai masana da ke kallon wannan taro daga nesa da sauran al’umma sun zuro ido su ga ta inda za a bullowa wannan babar matsala da ta addabi kowa da kowa a wannan yanki na arewacin Nijeriya tare da fatan cewa za ahada hannu da gwamnatoci domin yin aiki baki daya.