Zuwa yanzu wadanda suka halaka a girgizar kasar da ta auku a kasar Afghanistan sun zarce mutum 920, wdanda suka kuma jikkata sun haura 600, kamar yadda wani Babban Jami’i Gwamnati ya sanar.
“Wannan kididdiga na farko ne zai kuma iya cigaba da karuwa,’’ kamar dai yadda mataimakin Ministan Gwamnatin Taliban mai kula da tallafin gaggawa, Mawlawi Sharafuddin Muslim, ya bayyana a taronsa da manema labarai a garin KabuI.
A sakon ta’aziyyar da shugaban Gwamnain Taliban ya bayar tunda farko ya ce, mutum 300 suka mutu yayin da fiye da mutum 500 suka jikkata a balain.
Girgizar kasar mai karfin 6.1 ta shafi yankunan Paktika da Khost, ba a iya tantance yawan gidanjen da girgizar kasar ta shafa ba saboda girmar lamarin a halin yanzu. A wasu wuraren dukkan kauye gaba daya ya rushe.
A halin yanzu jami’ai a Kabul sun bayar da umarnin a yi amfani da jirgin sama mai saukan ungulu tare da motocin daukar marasa lafiya don ceto al’umma daga baraguzan gine-gine.
Jami’an majalisar dinkin duniya a Afghanistan sun bayyana cewa, a halin yanzu suna nan suna tantance tsananin abin da ya faru don sanin yadda za su kai taimako kamar yadda ya kamata.