Dan takara Gwamnan Jihar Zamfara a jam’iyyar PDP, Hon Dauda Lawal Dare, ya koka kan yadda wasu ke neman kawo zaben cikas a wasu runfunan zabe a fadin Jihar a ranar Asabar.
Dare ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala kada kuri’arsa a mazabarsa da ke Woman Center mai Lanba 0012 Gundumar Madawaki a cikin karamar hukumar Gusau a Jihar Zamfara.
- An Harbe Tsohon Kansila Har Lahira Kan Zargin Sace Akwatin Zabe A Kano
- Shugaban Majalisar Dattawa Ya Lallasa PDP A Mazabarsa Ta Katuzu
Dauda ya tabbatar da samu rahotannin cewa, “Wasu ‘yan jam’iyyar da suka ga ba za su samu nasara ba na neman tada kayar baya don su kawo zaben cikas a fasa kowa ya rasa.”
Dauda Lawal ya jinjina da yadda jama’a suka fito domin kada kuri’arsu kana ya yaba wa hukumar zabe bisa tsare-tsaren da aikin zaben ya gudana a saukake.
Ya kuma nuna kwarin guiwar na samun gagarumar nasara a zaben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp