Hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire a Yammacin Afrika (WAEC) ta Nijeriya ta sanar da cewa ta kwace lasisin makarantu 574 da aka samu da laifin aikata maguɗi a jarrabawar.
Hukumar ta bayyana cewa waɗannan makarantu ba za su iya gudanar da jarrabawa ba, koda yake jarrabawar 2025 (WASSCE) kuma za a fara ta ne daga Alhamis, 24 ga Afrilu, 2025.
- Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Yi Aiki Tare Don Daidaita Mummunan Yanayi A Yankin Manyan Tabkuna Na Afirka
- WAEC Ta Samar Da Hanya Mai Sauri Wajen Sake Zana Jarrabawar WASSCE Ga ÆŠaliban Da Suka Yi TuntuÉ“eÂ
Shugaban Ofishin WAEC na Nijeriya, Dr. Amos Dangut, ya bayyana hakan a cikin wani taron manema labarai a ranar Alhamis a shalƙwatar hukumar da ke Legas. Dangut ya ce WAEC ta tura jerin sunayen makarantu da aka soke lasisin su zuwa ga gwamnatin tarayya. Ya ƙara da cewa, wannan mataki ya shafi dukkanin cibiyoyin jarrabawa, inda aka tabbatar da cewa ba za a gudanar da jarrabawa a cikin waɗannan makarantu ba.
Dangut ya bayyana cewa adadin É—aliban da suka yi rijista don rubuta jarrabawar WASSCE ta 2025 ya kai 1,973,253 daga makarantu 23,554, inda 979,228 daga cikinsu suka kasance maza, 994,025 kuma mata.
Ya kuma bayyana cewa hukumar tana amfani da fasaha wajen inganta gudanar da jarrabawar, wanda ya haɗa da gabatar da jarrabawar WASSCE na kwamfuta (CB-WASSCE) na farko. Dangut ya ƙara da cewa wannan mataki na kawo canji yana daga cikin ƙoƙarin tabbatar da nagarta da gaskiya a cikin tsarin ilimi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp