Ran 10 ga watan Afrilu na shekarar 2024, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Ma Ying-jeou, tsohon shugaban jam’iyyar KMT na yankin Taiwan, inda suka nanata wajibcin tabbatar da dunkulewar kasar da hadin gwiwar bangarorin biyu wajen farfado da al’ummar Sinawa tare.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Joe Biden a Lima hedkwatar kasar Peru, inda Biden ya bayyana matsayin gwamnatinsa na nacewa da aiki da manufar “kasar Sin daya tak a duniya” da kin amincewa da ware yankin Taiwan daga babban yankin Sin.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a lardin Fujian, inda ya nanata muhimmancin fitar da sabuwar hanyar raya bangarorin biyu na mashigin tekun yankin Taiwan tare, da gaggauta cudanyar al’adu tsakaninsu, ta yadda za su kara amincewa da juna da yayata al’adun Sinawa da kara biyayyarsu ga kasarsu.