An zartas da rahoton binciken iznin halartar wakilai zuwa babban taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC karo na 14, a yayin taro karo na 39 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar karo na 13, inda aka tabbatar da iznin wakilai 2977, daga baya zaunannen kwamitin ya sanar da sunayen wakilai wadanda za su halarci babban taron majalisar karo na 14.
Wakilan da za su halarci babban taron suna wakiltar moriya da muradun al’ummun Sinawa, kuma za su tafiyar da ikon mulkin kasa bisa doka, ana iya cewa, suna sauke babban nauyi dake bisa wuyansu, don haka gudanar da aikin zaben wakilai yana da babbar ma’ana.
Rahoton da zaunannen kwamitin majalisar ya fitar ya nuna cewa, wakilan da aka zabar dukkansu suna goyon bayan jagorancin JKS da tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, kuma suna martaba dokokin kasa, suna kuma cudanya da jama’ar kasar yadda ya kamata, tare kuma da samun amincewarsu. (Mai fassarawa: Jamila)