Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa a wannan fili namu na Ado Da Kwalliya.
A yau shirin namu zai kawo muku yadda Uwargida ya kamata ta gyara danta kamar jariri daga haihuwa zuwa shekara biyu haka saboda a wannan lokacin ne yaro yake bukatar kulawar uwa saboda duk wani abu da zai zamantu ya bata yaro to zai iya zamo masa illah ajikin sa ko kuma cuta.
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance
- Yadda Zaben 2023 Zai Bambanta Da Sauran Zabukan Nijeriya
Shi karamin yaro yana bukatar kulawa sosai da zarar kika ga danki ya baci to yi sauri ki gyara ko jikinsa ko kuma tufafinsa ko muhallinsa wato inda yake, ba’a barin yaro da tufafi mai datti ko jikakkiya za su iya zamo illa a jikinsa saboda shi yaro komai ya samu baki yake kai wa, to ta nan ne zai iya haduwa da cuta.
Akwai wani kuskure da muke yi shi ne sai ka ga uwa za ta fita da yaro amma ba za ta iya daukar masa wani kaya ba ko da ya bata na jikinsa, sai ki ga uwa tana cewa ai ban zo da wani ba kaya ba zaka zauna da shi kwa haka, amma idan kin san kina da wani edtra da za ki canja masa musamman ma karamin yaro kamar jariri ya kamata uwa idan za ki fita da jaririnki kamar daga haihuwa zuwa shekara daya, ya zama kin yi tafi- da-gidanka wato ki samu wata za ka haka ya zamana komai kin sa a cikin wannan jakar kina da shi kome yaronki ya bukata kina da shi ba sai hankalinki ya tashi ba, “ba ni da kaza ina zan samu yaro yana neman kaza?”
In kin hada kayanki ba ki da bukatar haka misali: ki zama kin dau pampers akalla kamar karin guda biyu, haka ma tufafi shima ki dau kamar biyu kin sa masa ruwan shansa, shima ba sai kin nemi ruwa ba, sannan ya zama kina da ‘Paracetamol’ a cikin jakar saboda sai ki ga nan da nan jikin yaro ya yi zafi kafin ki dawo gida ko kuma idan asibiti za ki kika bashi wannan ‘Paracetamol’ zai dan samu sauki, sannan su wani harka matarin yawun yaro shima ya zama kin sa shi mai dan yawa saboda kar ya zo ya yi ta jika kirjinsa sanyi ya kama shi komai da kika san kina amfani ma yaronki, idan za ki fita ya kamata ki sa a jaka saboda kar ki zo kina nema.
Kema kanki idan kina kula da tsafta danki za ki ga kina burge kanki kuma danki kowa yana son daukarsa, za ki ga yana farin jini a wajen jama’a. Saboda haka don Allah iyaye mata mu kula ba sai kin fita inda kika ka je ana kyankymin ki ke da danki ba.