Wata babbar tawagar gwamnatin tarayya ta isa birnin Landan don fara shirin dawo da gawar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan jinya mai tsawo.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ta sauka a Ingila da safiyar Litinin don sa ido kan shirye-shiryen dawo da marigayin zuwa Nijeriya.
- Tinubu Ya Tabbatar da Rasuwar Buhari, Ya Tura Shettima Zuwa Landan
- Rasuwar Buhari: Gwamnatin Katsina Ta Ayyana Yau Litinin A Matsayin Ranar Hutun Aiki A Jihar
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar da Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne suka tarbe su a filin jirgin saman ƙasar.
Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya tabbatar da isar tawagar, yana mai cewa an karɓi umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na Shettima ya jagoranci shirye-shiryen dawo da gawar Buharin da kuma tsare-tsaren jana’izarsa.
Shugaba Tinubu ya bayyana jimaminsa a ranar Lahadi, ya kuma bayar da umarnin da a sauko da tutar Nijeriya ƙasa da rabin sanda a ko’ina a ƙasar, don girmama marigayin shugaban ƙasa Buhari.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa marigayi Muhammadu Buhari (Mai Ritaya), GCFR, ya shugabanci Nijeriya a matsayin shugaban soja daga 1984 zuwa 1985, sannan ya sake dawowa a matsayin zababben shugaban ƙasa daga shekarar 2015 zuwa 2023. Ya rasu a wani asibiti a birnin Landan bayan doguwar jinya a ranar Lahadi, 13 ga Yulin 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp