Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi masa tambaya game da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da ta gudana tsakanin bangaren Sin da na Amurka. Game da haka, Guo ya bayyana cewa, bisa jagorancin muhimmiyar matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, bangarorin biyu sun shiga tattaunawa mai ma’ana, mai zurfi, kuma mai amfani, kan muhimman batutuwan tattalin arziki da cinikayya, inda suka cimma matsaya daya kan abubuwan da suka mai da hankali a kansu. Bangarorin biyu sun kuma amince su kara kammala wasu muhimman ayyuka, da kuma aiwatar da matakan zartar da su a cikin gida.
Dangane da jirgi mai saukar ungulu na sojoji, da jirgin sama na yaki na Amurka, wadanda suka yi hatsari a tekun kudancin Sin, Guo ya bayyana cewa, Sin a shirye take ta samar da taimakon da ya dace ga Amurka bisa manufar jin kai. Ya ce Sin tana jaddada cewa, jiragen saman na Amurka sun fadi ne a lokacin atisayen soja a tekun kudancin Sin.
Jami’in ya ce Amurka ta sha tura jiragen ruwa, da jiragen sama masu yawa zuwa tekun kudancin Sin don nuna karfinta, wanda hakan ne tushen matsalolin tsaron teku, wanda ke haifar da cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Guo, ya kuma yi bayani game da shirye-shiryen ziyarar mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, a kasashen Saudiyya, da Kuwait, da Qatar, inda zai halarci taron kolin duniya karo na biyu na ci gaban zamantakewa.
Bugu da kari, dangane da dandalin tattaunawa na “Lanting” da ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar a yau, bisa taken “Inganta tsarin shugabancin duniya, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ta daukacin bil’adama”, Guo Jiakun ya ce manufarsa ita ce tattauna yadda za a inganta tsarin shugabancin duniya, da kuma tinkarar kalubalen duniya yadda ya kamata, tare da masana daga kasashe daban-daban. (Safiyah Ma)














