Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya yi jawabi a wajen bikin kaddamar da “kiran MDD ga Afirka a fannin dakile ayyukan ta’addanci cikin hadin-gwiwa” a jiya Alhamis, inda ya yi kira da a inganta kwarewar nahiyar, a fannin dakile ta’addanci, gami da kawar da tushen faruwar hakan.
Dai ya ce, shawarar tabbatar da tsaron duk duniya da kasar Sin ta gabatar, ta maida marawa kasashen Afirka baya, wajen kawar da ta’addanci a matsayin wani muhimmin bangare, da taimakawa MDD wajen kara taka rawa a fannin yakar ayyukan ta’addanci a duniya. A ‘yan shekarun nan, kasar Sin tana kara samar da goyon-baya ga hukumomin dakile ta’addanci, ta asusun shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba na Sin da MDD, ciki har da ofishin yakar ta’addanci na MDD.
Ya ce kasar Sin tana kuma nuna kwazo wajen halartar “kiran hadin-gwiwa”, da zurfafa hadin-gwiwa da hukumomin MDD, karkashin tsarin dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC, gami da asusun shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba na Sin da MDD, a wani kokari na kara samar da goyon-baya ga ayyukan dakile ta’addanci a Afirka.
A ranar Alhamis kuma, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD, Zhang Jun, ya gabatar da nasa jawabin, yayin muhawarar babban taron duba tsare-tsaren yaki da ta’addanci na duniya karo na 8, inda ya jaddada cewa, bai dace a dauki ma’auni biyu wajen yakar ta’addanci ba.
Zhang ya ce, har yanzu ta’addanci babban kalubale ne dake haifar da barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Don haka ya dace a inganta hadin-gwiwar kasa da kasa a wannan fanni ba tare da bata lokaci ba. Zhang ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon-bayan MDD wajen taka rawar bada jagoranci, ta yadda za’a kara samun zaman lafiya, kana al’ummun kasa da kasa za su iya kara more rayuwar su cikin kwanciyar hankali. (Murtala Zhang)