A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne wasu gungun fusatattun matasa suka kai wa ɗan majalisar dokokin jihar Kano Abdul-Majid Umar hari a wani taron da ya samu halartar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero.
Lamarin ya faru ne a wajen addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan marigayi Sheikh Isyaka Rabi’u da ke unguwar Goron Dutse a cikin birnin Kano. Hon. Umar wanda ke wakiltar ƙaramar hukumar Gwale a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP ya halarci zaman addu’ar wanda Sarki Aminu Aminu Ado shi ma ya halarta.
- Jihar Kano Na Shirin Gudanar Da Zaben Ƙananan Hukumomi – Gwamna Abba
- An Kama Wanda Ya Kitsa Kashe Janar Udokwere A Kano
Lamarin dai ya ta’azzara ne yayin da wasu da suka halarci taron suka zargi Ɗan Majalisar da goyon bayan dokar da ta kai ga tsige Aminu Ado daga karagar mulki.
Daidai lokacin da Ɗan majalisar ya ke shirin barin wurin taron,ya bayyana cewa wasu mutane ɗauke da muggan makamai sun kai masa farmaki bayan ya fita, amma ya yi nasarar tserewa ta hanyar shiga cikin motar jami’an ‘yansanda, amma ya ce wasu daga cikin magoya bayansa sun jikkata a farmakin.
Mai taimaka wa Sarkin kan harkokin yaɗa labarai, Khalid Adamu, ya musanta batun inda ya ce “babu wani daga cikin magoya bayan Sarki Aminu Ado da ke ɗauke da makamai”
Sai dai an rawaito cewa ta kai ga kafin fitar Ɗan Majalisar har sai da Sarki Aminu da kan shi ya tsawatar wa wasu daga cikin dogarawansa lokacin da suke shirin ƙaddamar wa da Ɗan Majalisar, kafin daga bisani ya yanke shawarar ficewa daga wurin taron.