A jiya Alhamis ne Chen Xu, wakilin kasar Sin a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland, ya jaddada kiran da kasar Sin ta yi na tsagaita wuta cikin gaggawa a zirin Gaza.
Yayin da zirin Gaza ke fuskantar matsalar jin kai mara misaltuwa, tsagaita bude wuta cikin gaggawa ita ce bukatar al’aummar duniya, kuma muhimmin mataki na samar da zaman lafiya, a cewar Chen yayin da yake karin haske kan matsayin kasar Sin kan halin da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra’ila a zaman taro na 55 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD.
- Kasar Sin Na Kokarin Samar Da Hidimomin Biyan Kudi Masu Sauki Ga Baki
- Kasar Sin Na Kokarin Samar Da Hidimomin Biyan Kudi Masu Sauki Ga Baki
Chen ya kara da cewa, kasar Sin tana kira ga Isra’ila da ta ba wa kungiyoyin agaji damar samun kudaden da suke bukata don gudanar da ayyukan ceto a Gaza da kuma aiwatar da matakan wucin gadi da umarnin kotun duniya yadda ya kamata.
Shawarar samar da kasashe biyu ita ce matsayar gama-gari na kasashen duniya da kuma hanyar da ta dace don tabbatar da zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila, a cewar Chen. Yana mai kira ga dukkan kasashen da su yi kokari don tabbatar da faruwar hakan. (Muhammed Yahaya)