Wakilin kasar Sin ya gabatar da jawabi, a gun taron kwamitin kare hakkin bil’adama na MDD karo na 51 a jiya Jumma’a, inda ya yaba da kokarin kasar Burundi, na ingantawa, da kare hakkin bil’adama, ya kuma nuna adawa da tsoma baki cikin harkokin gidan Burundi, ta hanyar fakewa da kare hakkin bil’adama.
Wakilin na kasar Sin ya bayyana cewa, a ko da yaushe, kasar Sin tana ba da shawarar cewa, ya kamata a kawar da bambance-bambancen da ke tattare da batun kare hakkin dan Adam, ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa, tare da adawa da siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam.
Ya ce wasu kasashe sun yi wa Burundi kazafi bisa bayanan karya, sun kuma yi amfani da kwamitin kare hakkin bil’adama a matsayin wani makamin siyasa, na tinkarar kasashe masu tasowa, da kara rura wutar gaba da juna, wanda hakan ba ya taimakawa wajen warware matsalar.
Don haka ya kamata, kwamitin kare hakkokin dan Adam ya kiyaye ka’idojin kaucewa wariya da siyasantar da batutuwa, da kuma yin watsi da “ma’auni iri biyu”, kana da mutunta hanyar ci gaban hakkin dan Adam da jama’ar Burundi suka zaba da kansu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)