A jiya Alhamis ne zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Zhang Jun ya yi kira ga kasashen duniya da su magance tushen matsalar karancin abinci.
Wakilin ya shaida wa taron kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya a budadden muhawara kan yunwa da rikice-rikicen dake haifar da karancin abinci a duniya cewa, wadanda suka fi fama da matsalar karancin abinci su ne, ba tare da togiya ba, kasashe masu tasowa. Matsalar karancin abinci ta samo asali ne sakamakon karanci da kuma rashin daidaiton ci gaban wasu kasashe a duniya, kuma hakan yana nuna tazarar dake tsakanin kasashe da suka ci gaba da kasashe masu tasowa.
Ya kara da cewa matsalar “Tana da alaka ta kut-da-kut da tsarin samar da abinci da cinikayya da aka dade a kai, da rashin adalci a tsarin mulkin duniya baki daya. Ya kamata kasashen duniya su magance matsalar karancin abinci daga alamomin har zuwa tushe, da inganta dokoki da ka’idoji, da daukar matakan da suka dace don cimma burin yaki da yunwa a shekarar 2030 kamar yadda aka tsara.” (Yahaya Babs)