• English
  • Business News
Sunday, August 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Yi Watsi Da Ikirarin Fifita Wasu Al’adu Da Cin Karo Na Wayewar Kai

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Yi Watsi Da Ikirarin Fifita Wasu Al’adu Da Cin Karo Na Wayewar Kai

Dai Bing, China's deputy ambassador to the United Nations, speaks during a Security Council meeting at United Nations headquarters, Friday, Feb. 24, 2023. (AP Photo/Seth Wenig)

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mukaddashin jakadan kasar Sin a MDD Dai Bing ya fada jiya Jumma’a cewa, tilas ne a yi kokarin yin fatali da da’awar da suka hada da fifita wasu al’ummomi da cin karo da wayewar kai.

Dai Bing, ya shaidawa babban taron bikin tunawa da ranar yaki da nuna kyamar musulunci ta duniya karo na farko, wanda ministan harkokin wajen kasar Pakistan Bilawal Bhutto Zardari da shugaban babban taron MDD Csaba Korosi suka shirya cikin hadin gwiwa, a hedkwatar MDD dake a birnin New York na kasar Amurka cewa, idan har ana son a yi yaki da nuna kyama da addinin Islama, da farko, wajibi ne mu tabbatar da daidaito. Kowane wayewar kai da addini yana da muhimmanci, kuma babu wanda ya fi wasu. Haka kuma tilas ne mu yi watsi da ikirarin nuna fifiko ga wasu wayewar kai da ma cin karo da wayewar kai.

Ya ce, wajibi ne mu taimakawa kasashe wajen zabar hanyoyin ci gaba da suka dace da yanayin kasashensu, da samar da ci gaba da zai shafi kowa, da nuna adawa da mayar da wasu saniyar ware, da sanya takunkumi na kashin kai.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kawar da “guba” masu kyamar addinin musulunci a yayin taron da aka shirya game da ranar yaki da nuna kyama ga addinin musulunci ta duniya. Yana mai cewa, tilas ne mu fahimci bambanci, ba wai a matsayin barazana ba, amma a matsayin wadatar al’ummominmu. Wannan yana nufin bunkasa harkokin siyasa, da al’adu da tattalin arziki a cikin hadin gwiwar zamantakewa. (Ibrahim)

Labarai Masu Nasaba

CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Dan Shekara 13 Ya Harbe Karamar Yarinya Da Bindiga A Ogun

Next Post

Mijina Ba Ya Son Haihuwa, Ko Ya Halatta Na Hana Shi Kaina? (Fatawa)

Related

CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu
Daga Birnin Sin

CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

15 hours ago
Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO
Daga Birnin Sin

Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

16 hours ago
CMG Ya Kaddamar Da Gangamin Tattara Fina-Finai Da Talabijin Da Aka Samar Bisa AI A Los Angeles
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Gangamin Tattara Fina-Finai Da Talabijin Da Aka Samar Bisa AI A Los Angeles

17 hours ago
Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba
Daga Birnin Sin

Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

18 hours ago
Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

19 hours ago
Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

2 days ago
Next Post
Mijina Ba Ya Son Haihuwa, Ko Ya Halatta Na Hana Shi Kaina? (Fatawa)

Mijina Ba Ya Son Haihuwa, Ko Ya Halatta Na Hana Shi Kaina? (Fatawa)

LABARAI MASU NASABA

An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato AK-47 A Kebbi

August 24, 2025
Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP

Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP

August 24, 2025
Trump Ya Ce Zai Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganawa Da Putin Da Zelensky Lokaci Guda

Trump Ya Ce Zai Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganawa Da Putin Da Zelensky Lokaci Guda

August 24, 2025
Fabio Na Brazil Ya Kafa Sabon Tarihi A Kwallon Kafa

Fabio Na Brazil Ya Kafa Sabon Tarihi A Kwallon Kafa

August 24, 2025
Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

August 24, 2025
NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

August 23, 2025
Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari

Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari

August 23, 2025
CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

August 23, 2025
Yadda Ake Alale

Yadda Ake Alale

August 23, 2025
Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.