Ƙungiyar ‘yan Jaridu (NUJ), ta ƙasa reshen jihar Kebbi, ta taya zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar wakilan kafofin yaɗa labarai, murnar nasarar lashe zaɓe, da buƙatarsu da su martaba dokoki ƙungiyar NUJ a jagorancinsu.
Cikin wata takardar da Sakataren NUJ reshen jihar kebbi, ismail Adebayo, ya fitar ƙungiyar ta yaba wa shugabannin da suka kammala wa’adinsu kan irin kokari da suka yi na kawo ci gaba ga gareta tare da alfahari da su.
- An Yi Hasashen “Ne Zha 2” Zai Zama Fim Na Kagaggun Hotuna Mafi Samun Kudi A Duniya
- Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39
Sababbin shugabannin wakilan reshen ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labaran an zaɓesu ne a ƙarƙashin kulawar wakilin uwar ƙungiya ta jihar a yammacin ranar Talata, inda Kabiru Wurma, na Kamfanin Jaridar LEADERSHIP ya yi nasara zama shugaba, da Muhammad Lawal na Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya (NAN), a matsayin Mataimakin Shugaba.
Sauran waɗanda suka samu nasarar sun haɗa da Olarenwaju Lawal, na jaridar Sun, a matsayin sakatare, sai Zubairu Tatu na Jarida Authority a matsayin sakataren kuɗi, sai Binta Aliyu Abdullahi da ta zama mataimakiyar sakatare, sai Umar faruk Abdullahi na LEADERSHIP HAUSA a Matsayin mai binciken kuɗi, Aminu Umar na Jaridar Legacy, a matsayin ma’ajin kudi.
Kungiyar NUJ reshen jihar ta buƙaci sabbin shugabannin da aka zaba da su tabbatar da suna amfani da dokokin tsarin mulkin ƙungiyar yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum. Uwar kungiyar kuma ta yi musu fatan alhairi wajen gudanar da kyakyawan jagoranci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp