Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da mummunan fashewar wata tankar man fetur a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 17 ga watan Oktoba, Simão ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma gwamnati da al’ummar Nijeriya.
Fashewar wadda ta afku cikin muni ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya yi matukar barna.
Simão ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda bala’in ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp