Bisa gayyatar bangaren Amurka, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, wato mataimakin shugaban kasa Han Zheng zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump, a ranar Litinin 20 ga watan nan a Washington D.C.
Wata sanarwa daga kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce Sin na bin ka’idojin mutunta juna, da zaman jituwa, da hadin gwiwar cimma moriya tare, a mahangarta, da matakanta na bunkasa alaka da Amurka.
Sanarwar ta kara da cewa, “A shirye muke mu yi tsaiwa tsayin daka tare da sabuwar gwamnatin Amurka, don inganta shawarwari da tattaunawa, da shawo kan banbance-banbance, da fadada hadin gwiwar cimma moriyar sassan biyu, da hada gwiwa wajen samar da alaka bisa daidaito, da karko kuma mai dorewa. Kana da zakulo hanya mafi dacewa da kasashen biyu za su bi, don wanzar da kyakkyawar hulda tsakaninsu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp