Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, daga ranar 9 zuwa 12 ga wata, wakilin musamman na shugaba Xi Jinping, Zhang Guoqing zai tafi kasar Faransa domin halartar taron koli kan ayyukan fasahar kirkirarriyar basira ta AI, bisa gayyatar da mai karbar bakuncin taron ta yi masa.
Zhang mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma mai mukamin mataimakin firaminista a majalisar gudanarwar kasar Sin.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, ta hanyar halartar taron, kasar Sin tana fatan karfafa cundayar juna da mu’amala da dukkan bangarori, da samar da daidaito kan hadin gwiwa, da kara matsa kaimi ga aiwatar da yarjejeniyar MDD kan fasahar zamani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)