A yau Litinin ne aka bude taron sauyin yanayi na MDD karo na 29 a birnin Baku, fadar mulkin kasar Azerbaijan. A bangaren tsagin kasar Sin, an gudanar da tattaunawa, inda a lokacin sabon wakilin musamman na kasar Sin game da batun sauyin yanayi Liu Zhenmin, ya yi karin haske game da shigar Sin harkokin da suka shafi jagorancin shawo kan sauyin yanayi, da yadda take taimakawa kasashe masu raunin ci gaba, da kananan tsibirai masu tasowa, da dabarun bunkasa amfani da makamashi da ake iya sabuntawa, da inganta karfin su na tunkarar tasirin sauyin yanayi.
A cewar Liu Zhenmin, ya zuwa karshen watan Yunin shekarar 2024, Sin ta sanya hannu kan kundi 52, masu nasaba da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, don gane da sauyin yanayi tare da kasashe masu tasowa 42, kana ta aiwatar da jerin tallafi, da musaya tare da su, ta kuma tallafawa kasashe masu tasowa da dabarun kyautata karfin su, da aiwatar da ayyukan kyautata kwarewar aiki sama da 300, ta kuma gudanar da kwasa-kwasai sama da 10,000 ga al’ummun kasashe masu tasowa sama da 120. (Mai fassara: Saminu Alhassan)