Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a yau cewa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), Jiang Zuojun ya tafi kasar Namibiya Alhamis din nan domin halartar jana’izar marigayi shugaba Hage Geingob da za a gudanar a birnin Windhoek.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp