Yayin taron watan Yuni na manyan wakilan kasashe mambobin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA, wanda ke gudana yanzu haka a birnin Vienna na kasar Austria, an tattauna game da yarjejeniyar mallakar jiragen karkashin ruwa na yaki masu amfani da makamashin nukiliya, wadda kasashen Australia, da Birtaniya da Amurka, wato AUKUS suka kulla.
Bisa mara bayan bangaren kasar Sin, manyan jami’an kasashen da suka halarci taron na wannan karo, sun yi musayar ra’ayoyi a karo na takwas a jere, a matsayi na tattaunawa tsakanin sassan gwamnatoci daban daban.
Da yake tsokaci kan batun a jiya Alhamis, wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar ta IAEA Li Song, ya yi fashin baki game da yarjejeniyar hadin gwiwar ta AUKUS, yana mai jaddada sarkakiya, da sa-in-sa da yarjejeniyar ke haifarwa. Jami’in ya kuma yi kira ga daukacin sassan dake da ruwa da tsaki a batun yarjejeniyar da su hada hannu waje guda, wajen ingiza matakan tattaunawa kan lamarin karkashin laimar IAEA, su kuma aiwatar da manufofin cudanyar dukkanin sassa a fayyace.
Wakilai daga kasashe sama da 20, ciki har da na Rasha, da Pakistan, da Masar, da Afirka ta kudu, da Indonesia, da Brazil da Argentina, sun tofa albarkacin bakin su yayin zaman na wannan karo, inda suka jaddada matsayin kasar Sin da ma shawarwarin da ta gabatar. Sun kuma yi kira da murya daya na kiyaye tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa da ma dokokin kasa da kasa.
Wannan shi ne karo na takwas a jere da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ke yin la’akari da wannan batu, ta hanyar tattaunawa tsakanin gwamnatocin kasashen duniya, lamarin da ya sake dakile yunkurin kasashen Amurka da Birtaniya da Australia na tilastawa sakatariyar hukumar.
Wannan hadin gwiwa na “AUKUS” tana amfani ne kawai da hadin gwiwar karkashin ruwa ta nukiliya a matsayin hujja don amfani da kasar Australia a matsayin hanyar ciyar da dabarun siyasar Amurka gaba, da kwaikwayon dabarun NATO na haifar da rikice-rikice na yanki da kuma tunkarar yankin Asiya da Pacific, don biyan bukatu na kashin kai. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan, Ibrahim Yaya)