Babban wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya gudanar da taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York, jiya Litinin bisa agogon birnin, domin gabatar da muhimman tsare-tsare na wa’adin shugabancin kasar Sin a kwamitin sulhu, na wannan wata.
A cewar Fu Cong, a yayin wa’adin shugabancin kwamitin sulhu na MDD a watan nan, kasar Sin za ta mai da hankali kan ra’ayoyin bangarori daban-daban da gudanar da tsarin mulkin duniya, da kula da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yanayin da ake ciki a wasu kasashen Afirka.
Da aka tambaye shi game da samfurin kirkirarriyar basira ta DeepSeek, wanda wani kamfanin kula da fasahohin kirkirarriyar basira na kasar Sin ya fitar, Fu Cong ya jaddada cewa, kada a raina hazakar masu binciken kimiyya da fasaha na kasar Sin, domin DeepSeek ya jawo hankulan mutane a duniya, kuma ya sa wasu mutane cikin damuwa da tsoro, wanda ke nuna cewa, dakile fasahohi ba zai yi tasiri ba, kana wannan darasi ne da ya kamata kasashen duniya, musamman ma Amurka, su koya.(Safiyah Ma)