Wakilin dindindin na kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Fu Cong a ranar Alhamis ya bayyana cewa, shawarar inganta jagorancin duniya (GGI) wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta yi kyakkyawar nuna yadda za a jagoranci bunkasa ci gaban MDD a nan gaba.
Da yake jawabi a wani taron muhawara na kwamitin sulhu na MDD mai taken “Majalisar Dinkin Duniya: La’akari da Makomar Gaba” da aka gudanar bisa cika shekaru 80 da amincewa da Yarjejeniyar Kafuwar MDD a ranar 24 ga watan Oktoban shekarar 1945, Fu ya ce, kalubalen duniya na karuwa sosai, kuma tsarin gudanar da jagorancin duniya yana cikin mawuyacin hali, kana MDD ta hau kan wani siradi mai muhimmancin gaske.
Wakilin na kasar Sin ya jaddada cewa, shawarar GGI ta bayar da mafita daga kasar Sin wajen cike gibin da ake da shi a bangaren jagorancin duniya da kuma bunkasa kafa tsarin kasa da kasa na gaskiya da adalci. Shawarar ta yi daidai da manufofi da ka’idojin Yarjejeniyar Kafuwar Majalisar Dinkin Duniya, tana kuma da nufin karfafa hadin kai da kyakkyawan tsari a tsakanin kasashen duniya, kana tana neman samar da mafita mai inganci ga kalubalen da ake fuskanta a wannan zamanin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)











