Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Geng Shuang ya ce a halin yanzu, ayyukan ta’addanci da yaduwar ta’addancin na kara tsananta a duniya, haka kuma ana fuskantar yanayin yaki da ta’addanci mai tsanani a duniya.
Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya Lahadi, yayin da yake jawabi a taron kwamiti na shida na babban taron MDD karo na 80 mai taken “matakan yaki da ta’addanci”, inda kuma ya gabatar da shawarwari uku na kasar Sin kan yaki da ta’addanci.
Ya ce bangaren kasar Sin ya gabatar da kiran kiyaye tsaron duniya da na tafiyar da harkokin duniya, wadda ta yi kira ga kasa da kasa da su bi tunanin tafiyar da harkokin duniya bisa tushen shawarwari da raya kasa da more fasahohi tare, don tinkarar kalubalen duniya ciki har da yaki da ta’addanci. Kuma bisa wannan tunani, bangaren Sin yana kira ga kafa tsari daya don hada kan kasa da kasa wajen yaki da ta’addanci, da tabbatar da dokokin kasa da kasa don kyautata tsarin dokokin yaki da ta’addanci, da kuma kiyaye manufar tunanin aiki da hankali don hada gwiwa tsakanin kasa da kasa a fannin yaki da ta’addanci.
Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce da ta’addanci ya yi wa illa. Ya ce kungiyar ETIM wadda kwamitin sulhu na MDD ya ayyana a matsayin ta ta’addanci, ta taba tada rikice-rikicen ta’addanci da dama a cikin kasar Sin, kana ta gudanar da ayyukanta a kasar Syria, da Afghanistan da sauransu. Ya jaddada cewa, kasar Sin na kira ga bangarori daban daban da su dauki matakai don yaki da kungiyoyin ta’addanci ciki har da kungiyar ETIM. (Zainab Zhang)