Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi banayi kan kuri’ar da kwamitin sulhu na majalisar ya kada jiya Laraba dangane da tukunkuman kasar Sudan.
Bayan kada kuri’ar, Dai Bing, ya bayyana cewa, bisa hadin gwiwar dukkan bangarori, an samu ingantuwar yanayi a Dafur. Yana mai cewa, takunkuman da kwamitin sulhu na MDD ya kakabawa Sudan, sun riga sun zarce wa’adinsu, kuma ya kamata a dage su bisa yadda yanayi ke ingantuwa.
A cewarsa, takunkumai muhimman matakai ne da dokar MDD ta ba kwamitin sulhun. Kuma makasudinsu shi ne, samar da yanayin warware batutuwa a siyasance. Sai dai a zahiri, suna kara maye gurbin matakan diflomasiyya, har ma a wasu kasashe, a kan yi amfani da su a matsayin wata hanya ta matsin lamba.
A jiya ne kwamitin ya amince da kuduri mai lamba 2676 da kuri’u 13, inda kasashe biyu suka kauracewa kada kuri’ar. Kudurin na da nufin tsawaita aikin kwamitin kwararru mai taimakawa kwamiti mai kula da yanayin aiwatar da takunkumai a kasar ta Sudan, har zuwa ranar 12 ga watan Maris na 2024. Rasha da Sin ne kasashe biyu da suka kauracewa kada kuri’ar. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)