Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana jiya Alhamis cewa, cikin dogon lokacin da suka gabata, yanayi na ci gaba da tabarbarewa a yankin Falesdinu da aka mamaye, inda mutanen yankin suka sha fama da rikice-rikice, lamarin da ya kasance a matsayin abun damuwa sosai ga kasar Sin. Ya ce, ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya mai da matukar hankali kan batun, tare da daukar matakai masu dacewa, ta yadda za a hana ci gaba da illata yanayin yankin.
Zhang Jun ya bayyana haka ne a yayin taron tattaunawa kan matsalar Falesdinu ta yankin Gabas ta Tsakiya, na kwamitin sulhu na MDD. Ya kara da cewa, kasar Sin tana Allah wadai da dukkanin matakan soja da aka dauka kan fararen hula a yankin da aka mamaye, tana kuma yin kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kai zuciya nesa, domin magance tabarbarewar yanayi a yankin. Haka kuma, ya kamata bangaren da ya mamaye yankin, ya bi dokar kasa da kasa, da kuma hana sojoji da ‘yan sanda daukar matakan soja da ba su dace ba, da hana su kwace kadarorin fararen hula da lalata yanayin tsaronsu. Ya ce, Falesdinu da Isra’ila suna makwabtaka da juna tun da dadewa, ya kamata su tsayar da aikace-aikacen tashe-tashen hankula a tsakaninsu, da kuma hada kai wajen shimfida yanayin tsaro a yankin.
Bugu da kari, ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa, domin warware matsalar Falesdinu cikin lumana kuma bisa yanayi na adalci, ta yadda za a shimfida yanayin zaman lafiya na dindindin a yankin Gabas ta Tsakiya. (Mai Fassara: Maryam Yang)