Wakilin kasar Sin ya yi jawabi a wajen taro na 53, na kwamitin hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a jiya Alhamis, inda ya bukaci kasar Japan, da ta dora muhimmanci kan damuwar kasa da kasa, game da batun da ya shafi zubar da dagwalon ruwan makamashin nukiliya cikin teku.
Wakilin ya kara da cewa, har yanzu Japan ta kasa gabatar da shaidun dake nuna cewa, zubar da dagwalon ruwan nukiliya a teku, ba shi da wata illa. Kana, kididdigar da Japan ita kanta ta gabatar, ta shaida cewa, kusan kaso 70 bisa dari na dagwalon ruwan nukiliyar da aka riga aka tace har yanzu yana da illa.
Wakilin na Sin ya jaddada cewa, kudirin gwamnatin Japan, na zubar da dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, na da alakar kut da kut, da tsaron muhallin duniya, da lafiyar al’ummun kasa da kasa.
Don haka wannan ba harkar cikin gida ce ta Japan kadai ba, kana, ya kamata Japan ta dora muhimmanci sosai kan babbar muryar adawa daga cikin gida da waje, gami da damuwar kasa da kasa, da sauke nauyin dake wuyan ta yadda ya kamata, domin sarrafa dagwalon ruwan nukiliyar ta hanya mafi tsaro, da dacewa, kuma ba tare da wata rufa-rufa ba. (Murtala Zhang)