Sakamakon manyan hare-hare ta sama da Isra’ila ta kaddamar a zirin Gaza, wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya ce Sin ta yi matukar bakin ciki yadda aka lalata yanayin tsagaita bude wuta mai wahalar gaske da aka cimma a zirin Gaza. Kazalika, Sin na bayyana matukar damuwa, da yin Allah wadai da sake haifar da yakin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza.
Fu Cong, wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, a taron kwamitin sulhu kan batun Falasdinu da Isra’ila. Ya ce daukar matakan soja ba ita ce hanyar warware matsalar Falasdinu da Isra’ila ba. Kuma kasar Sin na fatan Isra’ila za ta yi watsi da aniyarta ta amfani da karfi, ta dakatar da ayyukan soji a zirin Gaza nan take, sannan ta daina azabtar da fararen hula dake zirin Gaza baki daya.
- El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja
Fu Cong ya ce, kasar Sin na matukar bukatar tsagaita bude wuta mai dorewa a zirin Gaza, tana kuma adawa da mayar da taimakon jin kai wani makami na yaki ko kuma siyasantar da batun. Kasar Sin ta bukaci Isra’ila da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta, game da mamayar da take yi, a karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa, tare da ba da damar ci gaba da shigar da kayayyakin jin kai zuwa zirin Gaza.
Fu Cong ya ce, kasar Sin na kira da a sake farfado da ra’ayin siyasa na kafa “kasashe biyu”, da kuma aiwatar da “manufofin kasashe biyu”, a matsayin hanya daya tilo da za a bi don warware batun Falasdinu.
Bugu da kari, Fu Cong ya bayyana cewa, bangaren Sin yana goyon bayan kwamitin sulhu na MDD, da ya ci gaba da daukar matakai na sa kaimi ga tsagaita bude wuta a zirin Gaza, da maido da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma warware batun Falasdinu cikin daidaito, da adalci da yanayi mai dorewa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp