Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Geneva Che Xu, ya yi jawabi a gun taron tattaunawa na shekara-shekara, kan gudummawar fasahohi karo na 59, na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD a jiya Juma’a, a madadin walikan kasashe fiye da 70, game da raya hidimomi ga nakasassu ta hanyar fasahar AI, inda ya yi kira ga raya fasahar AI don inganta fasahohi, da karfin hidimomin da ake samarwa nakasassu, da kuma sa kaimi ga sassan kasa da kasa, ta yadda za su iya more fasahohin bunkasa fasahar AI.
A cikin jawabin nasa, ya gabatar da shawarwari uku. Na farko ya ce kamata ya yi a mai da hankali ga bukatun dan Adam, da tabbatar da girmamawa, da kare hakkin dan Adam yayin da ake raya fasahar AI. Na biyu kuma a yi amfani da fasahar domin gajiyar dukkanin bil’adama, da sa kaimi ga samar da damar yin amfani da fasahar cikin adalci, da raya ta yadda ya kamata. Na uku kuma a wanzar da hadin gwiwa, da tabbatar da moriyar juna, da kara nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa a fannonin hada-hadar kudi da fasahohi, da kyautata ayyukan sarrafa fasahar AI a duniya, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin sassan kasa da kasa. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp