Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Geng Shuang, ya yi kira ga kasa da kasa, da su dauki wani mataki na magance tabarbarewar halin da ake ciki a kasar Ukraine.
A wajen wani taron kwamitin tsaron MDD da aka yi kan batun Ukraine a jiya Jumma’a, Geng ya ce, fada a Ukraine ya kara barkewa a kwanan nan, kuma ana kara fuskantar rashin sanin tabbas. Kasar Sin tana fatan bangarori masu gaba da juna, za su kara yin hakuri, kana gamayyar kasa da kasa su kauce ma daukar matakan da ka iya tsananta halin da ake ciki a kasar, musamman haramta amfani da makaman nukiliya, domin kada a haifar da matsalar da ba za’a iya daidaita ta ba.
Geng ya kara da cewa, ya dace a yi kokarin yin shawarwari. Kwanan nan, wata tawagar neman samun zaman lafiya dake kunshe da shugabannin wasu kasashen Afirka 6, ciki har da Afirka ta Kudu, sun ziyarci kasashen Ukraine da Rasha, kuma kasar Sin ta yi maraba da hakan. Ya ce, kasar Sin na fatan dukkan kasashe masu rungumar zaman lafiya da tsayawa kan adalci, za su iya samar da goyon-baya, ga neman samun sulhu da yin shawarwari. (Murtala Zhang)