Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi tir da harin dakarun Isra’ila kan wata cibiyar kiwon lafiya dake arewacin zirin Gaza. Jami’in ya yi sukan ne yayin taron gaggawa na kwamitin tsaron MDD game da batun Falasdinu da Isra’ila, yana mai kira ga Isra’ila da ta yi biyayya ga dokokin kasa da kasa, ta kuma dakatar da mayar da asibitoci fagagen yaki.
Fu Cong ya kara da cewa, wasu masu fashin baki sun nuna yadda muggan hare-haren Isra’ila kan cibiyoyin kula da lafiya a Gaza, suka jefa cibiyoyin cikin yanayi na kusan rushewa baki daya, wanda hakan wata dabara ce ta mayar da Gaza wuri da dan adam ba zai iya rayuwa cikinsa ba.
Jami’in ya ce Sin na matukar nuna damuwarta, da bayyana matukar adawa da hakan. A daya hannun kuma, Sin na kira ga Isra’ila da ta mutunta nauyin dake wuyanta na martaba dokokin kasa da kasa, ta dakatar da kaiwa cibiyoyin kiwon lafiya da ma’aikatansu hare-hare, tare da sakin jami’an lafiya da take tsare da su. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp