ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu

by Idris Aliyu Daudawa
2 years ago
ilimi

Jami’an ilimi kwararru ne a bangaren ilimi wanda aikinsu shi ne da alhakin bunkasawa, aiwatarwa,da kuma tsara manufofin ilimi da tsare tsare.Suna bada gudunmawa wajen tabbatar da cewa kowa yana samun ingantaccen ilimi mai nagarta. Jami’an ilimi sune yin aiki ne a wurare daban- daban da suka hada da hukumomin gwamnati, wuraren ko hukumomin da ba a kafa su saboda su samar da riba da kuma makarantun ilimi. Gudunmuwoyin  da jami’an ilimi suke badawa suna da yawa.

Suke da alhakin shirya bincike da kuma nazari domin su gano wuraren da suke da matsalolin da suka shafi ilimi, da kuma samar da hanyoyin da za ayi maganinsu. Hakanan ma jami’an ilimi suna samar da shawarar data kamata da kuma taimako ga Malamai da sauran masu harkar data shafi ilimi domin tabbatar da cewa suna bada nagartaccen ilimi ga dalibai.

  • Kidayar Jama’a Da Harkar Ilimi
  • Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Kudin Shiga Na Naira Tirililan 34.8 A 2025

Bugu da kari suna kuma taimakawa wajen samar da yadda za a tafiyar da lamari, tsara shi, da yadda za a gabatar horarwa,da rika bibiyar yadda ake aiwatar da duk wani taimakon da ake ba ilimi.Wannan ya hada bayan aikin su Malamai da kuma masana ilimi, jami’an ilimi har ila yau suna mu’amala da Malamai, dalibai da sauran masu ruwa da tsaki ta bangaren ilim.

ADVERTISEMENT

 

Suna aiki domin su kulla dankon zumunci da hadin gwiwa domin tabbatar da cewar ana biyan duk bukataun kowa. Hakanan ma su jami’an ilimin suna bada gudunmawa wajen  bibiyar yadda ake aiwatar da tsare- tsare da manufofin ilimi kamar yadda ya dace. Suna amfani ne da fasahar zamani da sauran wasu abubuwan da suka zama sheda domin gano wuraren da suke da bukatar da a kawo masu dauki, da daukar matakan da za su samar da canji.Maganar gaskiya jami’an ilimi suna da muhimmanci saboda tabbatar da kowa ya samu ilimi, babu bambanci mai kuma inganci.Ayyukansu na taimakawa wajen yadda ilimi zai iya kasancewa a gaba da kuma tabbatar da cewa dalibai sun samu  mizanin ilimin daya dace su samu.Duk hakan na kasancewa ta wajen samar da yadda ya dace a tafiyar da lamari, taimakawa, da jagoranci, jami’an  ilimi har ila yau suna samar da yanayi maikyu da yake bunkasa koyon ilimi ga masu koyo da ke koyawa ilimin. Digiri satifiket na shedar Ilimin ya kamata ace jami’in ilimi ya mallaka

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

 

Jami’in ilimi mutum ne wanda alhakin kulawa da ilimi ake aiwatar da shi tare da dukkan tsare- tsare ko manufofi suka  rataya a wuyansa, ko dai a wata hukuma ko kuma wurin da al’umma suke. Idan mutum na bukatar zama jami’in ilimi akwai bukatar ace  ya mallaki takardar shedar ilimi.Ko kuma a kalla yana da digiri na farko a sashen da ya shafi ilimi. Duk da hakan ma ana bukatar da yana da kwarewa ko ya taba aikin koyarwa ko kuma ilimin da yake da alaka da tafiyar da harkar mulki ya kan zama dole hakan. Idan ana maganar dabara kuma jami’in ilimi abin so ne ace ya mallaki ko yana da dabarar iya hulda da al’umma kwarai da gaske, domin kuwa zai rika hulda ne da mutane daban- daban da suka hada da Malamai, dalibai, Iyaye,da sauran masu fada aji ta bangaren  ilimi.Akwai bukatar su kasance sun san makamar tafiyar da manufofin ilimi da yadda za a aiwatar da su,da kuma samun mafita daga wasu.Su kasance sun nakalci da sanin yadda za a tafiyar da harkokin ilimi sosai.Ga kuma su iya tafiyar da ayyukan kan lokacin da aka ce masu,kai hara ma da su bunkasa da kuma tsare- tsare da manufofin ilimi.

ilimi
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026
ilimi
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
ilimi
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Next Post
Ko Me Ya Sa Amurka Ta Gaza Cimma Burinta Na Yakin Kimiyya Da Fasaha Da Kasar Sin?

Ko Me Ya Sa Amurka Ta Gaza Cimma Burinta Na Yakin Kimiyya Da Fasaha Da Kasar Sin?

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026
SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026
ilimi

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.