• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Sin Ya Yi Tir Da Matakan Matsin Lamba Da Nufin Dakile Tsarin Jagoranci Da Ci Gaban Duniya

by CGTN Hausa
2 years ago
Wakilin Sin

LABARAI MASU NASABA

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD, da sauran hukumomin kasa da kasa dake Vienna Li Song, ya yi Allah wadai da irin matakan matsin lamba da wasu sassa ke dauka, da nufin dakile managarcin tsarin jagoranci, da ci gaban duniya, wanda hakan ke haifar da koma bayan bunkasar zamantakewa da tattalin arzikin duniya.

Li wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin wani taron karawa juna sani mai taken “Matakan matsin lamba na kashin kai da mummunan tasirinsu ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin sassan kasa da kasa”. Ya kara da cewa, Sin na tsaiwa tsayin daka wajen bunkasa sadarwa tsakaninta da daukacin sassa masu ruwa da tsaki, kana tana da burin shiga a dama da ita, wajen wanzar da halastaccen ikon raya kasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa, kuma tana yayata dukkanin manufofi na hadin gwiwar kasashen duniya domin samar da ci gaba.

  • Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Raya Yankin Delta Na Kogin Yangtze 
  • Lallai A Rika Hukunta Masu Aikata Laifukan Zabe

Taron wani bangare ne na ayyukan babban taron hukumar raya masana’antu ta MDD ko UNIDO, wanda ke gudana tun daga Litinin har zuwa Juma’ar nan.

Albarkacin babban taron na UNIDO, ofishin wakilcin Sin na MDD dake Vienna, ya ce a jiya Alhamis kasashe 10 da suka hada da Sin, da Rasha, da Iran da Cuba, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa game adawar su da matakan matsin lamba da wasu sassa ke aiwatarwa, wadanda suka ce na kawo tarnaki ga burin da ake da shi na cimma nasarar ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan zuwa shekarar 2030, tare da dakile matakan dunkule dukkanin sassa, da wanzar da ci gaban masana’antun duniya. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka
Daga Birnin Sin

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Next Post
CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024

CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.