Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron karawa juna sani kan zurfafa hadin kai da raya yankin Delta na kogin Yangtze a Shanghai a ranar 30 ga watan Nuwamba, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.
Yankin Delta na kogin Yangtze yana taka muhimmiyar rawa a fannin kara azama kan samun daidaito wajen raya sassan kasar Sin. A matsayinsa na shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya sha jaddadawa a yayin wasu tarukan da aka yi a cikin gida da wajen kasar Sin cewa, kasar Sin ba za ta sauya aniyarta ta bude kofarta ga kasashen ketare ba, kana bunkasuwar kasar Sin za ta zama damarmaki ga kasashen duniya.
Sakamakon aiwatar da aikin raya yankin Delta na kogin Yangtze, ya sa yankin zama wata kyakkyawar kofar kasar Sin ga katare, lamarin da zai taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da hada-hadar kudi da kuma cinikayya a duniya. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp