Farfesa Jeffrey Sachs na jami’ar Columbia, ya yaba wa nasarorin da Sin ta samu, inda ya ce, “shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, wani shiri ne mai ban mamaki kuma na musamman.”
Farfesa Sachs ya fadi hakan ne a kwanan nan, yayin da wakiliyar rukunin gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG ta zanta da shi. Ya kuma bayyana cewa, kamar yadda shugaban kasar Xi Jinping ya fada a karon farko, yayin gabatar da wannan shawara, tushen ta ya samo asali ne daga hanyar kasuwanci ta hanyar siliki, hanyar dake da tarihin fiye da shekaru dubu biyu tsakanin yankin gabas da yamma. Ya ce, “Idan kina nazarin tattalin arziki kamar yadda nake yi, za ki yi imanin cewa, ainihin ciniki shi ne samun moriyar juna, da habaka al’adu, da samar da ingantattun kayayyaki, wanda ke amfanar mutane daga sassa daban-daban na duniya, to za ki amince cewa ciniki shi ne tsarin gaskiya na samun riba ga kowa. Ina goyon bayan wannan ra’ayi na hadin kai, kuma na yi imanin cewa yana da fa’ida mai yawa. Shirin Sin na tabbatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ cikin hadin gwiwa, ya yi kokari sosai a fannin inganta hadin kai da kara zurfafa mu’ammala.” (Amina Xu)