Wata wakiliyar matasan yankin musamman na Hong Hong na kasar Sin, Rong Shiyun, ta gabatar da jawabi a wajen taro na 53 na kwamitin hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, inda ta bayyana yadda Hong Kong ta samu ci gaba bayan da aka aiwatar da dokar tabbatar da tsaron kasa, kana, ta shaida cikakken goyon-bayan matasan yankin, ga manufar “kasancewar kasa daya amma tsarin mulki biyu”.
Rong Shiyun ta ce, manufar “kasancewar kasa daya amma tsarin mulki biyu”, ta sa Hong Kong ta iya more dimbin albarkatu gami da babbar kasuwa ta kasar Sin, a yayin da take iya ci gaba da bin tsarin zaman rayuwa da tattalin arziki irin nata. Bayan da aka aiwatar da dokar tabbatar da tsaron kasa a Hong Kong, zaman rayuwar al’umma ya koma hanya madaidaiciya, al’amarin da ya aza tubali mai inganci ga ci gaban yankin a nan gaba. Maganar da ake cewa, wai dokar tabbatar da tsaron kasa a Hong Kong ta illata halastaccen hakkin dan Adam a wurin, shafawa kasar Sin bakin fenti ne aka yi. Hakikanin gaskiya, akasarin kasashe na aiwatar da dokokin da suka shafi tsaron kasa, wanda shi ne babban tushen kare al’umma, da tabbatar da ci gaban tattalin arziki da zaman wadata. Rong tana kuma fatan kasa da kasa za su ci gaba da mutunta gami da nuna goyon-baya ga ra’ayoyin matasan yankin Hong Kong. (Murtala Zhang)