• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wanda Ya Shuka Zamba, Shi Zai Girbe Ta

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Zamba

“Mun yi karya da yaudara da sata, mun kuma samar da darussa na musamman na koyar da ayyukan, wadanda suka kasance abubuwan da muke alfahari da su na tabbatar da ci gaban kasar Amurka.” Kalaman tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ke nan, don gane da irin abubuwan kunya da Amurka ta aikata ba tare da boyewa ba a shekarun baya. Lallai a kan batun yaudara, Mr.Pompeo ya fadi gaskiya.

 

A kwanan nan kuma, a karon farko cikin shekaru 12, rundunar sojin Amurka ta wallafa tsarin tafiyarwa mai lakabin “Yaudara”, wato wani salo da ake amfani da shi wajen yaudarar abokan gaba da kitsa karairayi, matakin da ya ba kasashen duniya mamaki matuka.

  • Zanga-zanga: Birtaniya, Amurka Da Kanada Sun Gargadi ‘Yan Kasarsu Mazauna Nijeriya
  • Me Ya Sa Manyan Shugabannin Kamfanonin Amurka Ke Ziyaratar Sin A Wannan Lokaci?

A hakika, domin cimma burinta, har kullum Amurka ba ta jin kunyan aikata karya da yaudara da kuma sata, a maimakon haka, tana alfahari da su. Kuma ba a fannin soja kawai Amurka take yaudara ba, ma iya cewa hakan ya zame wa kasar jini da tsoka. Idan ba mu manta ba, a tsakiyar karni na 20, hukumar leken asiri ta CIA ta Amurka, ta fara aiwatar da shirin da aka san shi da suna “Operation Mockingbird”, shirin da ke yunkurin sayen ’yan jarida da wasu hukumomin kasa da kasa don samun bayanan sirri, kuma har zuwa yanzu, kana hukumar CIA ita ma tana kokarin sarrafa kafofin yada labarai ta hanyar sayen ma’aikatansu.

 

LABARAI MASU NASABA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Kaza lika a shekarar 2003, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Colin Powell, ya zargi kasar Iraki da nazari kan makamai masu guba, tare da nuna farin garin da ya samu a gun taron kwamitin sulhun MDD, kuma da wannan dalili ne sojojin hadin kai na Amurka da Birtaniya, suka kaddamar da yaki a kan Irakin, amma har zuwa yanzu, Amurka ba ta iya nuna hakikanin shaida mallakar makaman kare dangi a Iraki ba.

 

Ban da haka, Amurka ta kaddamar da yaki a kan Syria, bisa dalilin wai sojojin gwamnatin kasar sun yi amfani da makamai masu guba, amma ga shi sojojin kasar Amurka da ke Syria na satar albarkatun mai da alkama na Syria a kowace rana, tare da yin jigilarsu zuwa ketare.

 

Domin dakile kasar Sin kuma, Amurka ta yayata karairayi na shafa wa kasar bakin fenti, a kan manufofinta game da jihar Xinjiang, har ma ta yada karairayi game da alluran rigakafi da kasar Sin ta samar a yayin da ake fama da annobar COVID-19, ba tare da yin la’akari da lafiyar al’ummar kasashe masu tasowa wadanda ke tsananin bukatar rigakafin ba.

 

Irin wadannan abubuwa ba za su lissafu ba, wadanda suka kasance shaida ta “karya da yaudara da sata” da ’yan siyasar Amurka suka bayyana. Don haka abun tambaya a nan shi ne wace ce ke yada karairaiyi a fadin duniya, kuma wace ce ke gudanar da ayyuka na gurgunta fahimtar al’umma a kan wasu kasashe, kana kuma wace ce ke ta kutsen yanar gizo? Kasashen duniya sun san amsar hakan, kuma Amurka ta ci amana ta hanyar aikata munanan abubuwa.

 

Kamata ya yi Amurka ta daina yada karairayi, ta daina yaudarar al’ummar kasashen duniya, kuma ta daina shafa wa sauran kasashe kashin kaji. Kamar yadda Bahaushe kan ce, wanda ya shuka zamba, shi zai girbe ta! (Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 4, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Ra'ayi Riga

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 4, 2025
Next Post
Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Zai Laƙume ₦6.2tr – Godswill Akpabio Daga cikin Kasafin Bana

Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Zai Laƙume ₦6.2tr - Godswill Akpabio Daga cikin Kasafin Bana

LABARAI MASU NASABA

GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.