• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wanda Ya Shuka Zamba, Shi Zai Yi Girbinta

by CGTN Hausa
2 years ago
Zamba

Tun bayan da Japan ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya na tashar Fukushima cikin teku, kasar ta fuskanci matsala wajen sayar da abincin ruwanta. Bisa labaran da kafofin yada labarai na kasar suka bayar, an ce, a ma’adanai na wasu kamfanonin sarrafa abincin ruwa na kasar, tarin abincin ruwa na Scallop da dai sauransu sun kusan kai rufin ma’adanan da ke da tsayin mita 8. 

An ce, a shekarar bara, gaba dayan kudin abincin ruwa da Japan ta sayar ga kasashen duniya ya kai dala biliyan 1.97. Amma tun bayan da Japan din ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, yawan abincin ruwan da kasar ke sayarwa ga waje ya ragu da matukar yawa, har ma wasu masanan sun yi hasashen raguwar za ta iya kai kaso 50%. Ban da wannan, sakamakon yadda sassan kasa da kasa ke nuna kyamar matakin na Japan, harkokin yawon shakatawa na kasar ma na fuskantar munanan asarori.

  • Sakamako Da Aka Samu Bayan Gina Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya
  • Jamaica Na Neman Greenwood Ya Koma Wakiltarta A Kwallon Kasa

Sinawa kan ce “an tsinci ridi, a yayin da kuma aka yi watsi da kankana”, wajen bayyana yadda akan sha babbar hasara sakamakon neman cin karamar riba, to, abin da Japan ke yi ke nan yanzu, sakamakon yadda ta zubar da dagwalon nukiliyarta cikin teku don neman yin tsimin kudi, amma a sa’i daya, tana kashe makudan kudade wajen wanke kanta daga zarge-zarge da ake mata, tare kuma da shan munanan hasarori ta fannonin tattalin arziki. Lallai ma iya cewa, wanda ya shuka zamba, shi zai yi girbinta.

Tun daga ranar 5 ga wata, a zagaye na biyu ne Japan ta sake fara zubar da ruwan dagwalon nukiliyarta cikin teku, aikin da za ta shafe kimanin kwanaki 17 tana yi a wannan zagaye. Gaba dayan ruwan dagwalon nukiliya da ake ajiye da shi a tashar Fukushima ya kai sama da ton miliyan 1.3, kuma an yi hasashen za a shafe a kalla shekaru 30 kafin an zubar da gaba dayansa cikin teku. Don haka, da wuya mu iya hasashen yadda tekunan duniyarmu za su kasance, kuma ko halittun teku za su ci gaba da rayuwa ko a’a, da kuma yaya duniyarmu za ta kasance, da ma wace masifa matakin zai janyo wa dan Adam.

Muna yi wa gwamnatin Japan gargadi da ta dakatar da wannan mugun aikin nan da nan, kuma ta dauki matakan da suka dace, don kiyaye teku na dukkanin ’yan Adam. (Mai Zane:Mustapha Bulama)

LABARAI MASU NASABA

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 2, 2025
An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
Daga Birnin Sin

An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu

November 2, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
Next Post
Charles Onunaiju: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Sanya Sabon Ci Gaba A Nijeriya

Charles Onunaiju: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Sanya Sabon Ci Gaba A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya

November 2, 2025
An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu

An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu

November 2, 2025
Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?

Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?

November 2, 2025
A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?

A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?

November 2, 2025
Maganin Nankarwa (3)

Maganin Nankarwa (3)

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legas

November 2, 2025
Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka

Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka

November 2, 2025
Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala

Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.