Bayan taron manyan shugabanni na birnin Sharm el-Sheikh na kasar Masar a baya bayan nan, wanda ya kai ga sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, a yanzu haka hankula sun fara kwantawa, bayan tsawon lokaci da aka shafe ana jiran cimma wannan matsaya.
Ga bangarori da yawa, nasarar da aka cimma ta zamo babban abun alfahari mai faranta rai, amma a daya hannun akwai masu ganin har yanzu “akwai sauran rina a baka. A yayin da shugabannin gabas ta tsakiya ke kira ga Israila da ta martaba yarjejeniyar da aka cimma, a daya hannu Amurka na kira ga kungiyar Hamas ta Falasdinu da ta yi taka-tsantsan. Har ila yau, su ma dakarun Houthi na Yemen sun sha alwashin kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana, don tabbatar da Israila ba ta karya yarjejeniyar ba.
Ko shakka babu shekaru da dama da aka shafe ana fuskantar tashe-tashen hankula a gabas ta tsakiya, sun haifar da matukar koma baya ga kyawawan burikan al’ummun yankin game da wanzar da zama lafiya. Sai dai a halin yanzu, sassan kasa da kasa na fatan yarjejeniyar da aka cimma za ta banmbanta da makamantanta da suka gabata.
Kafin cimma nasarar hakan, an kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza fada da mamaya a Gaza, lamarin da ya haddasa asarar rayuka sama da 67,000, da barnata dukiyoyin da aka kiyasta darajarsu kan kusan dalar Amurka biliyan 70, kana an lalata kusan kaso 90 bisa dari na daukacin gine-ginen dake Gaza, baya ga al’ummun zirin sama da miliyan guda da suka rasa matsugunansu.
Ko shakka babu wannan yanayi ya haifar da wani rauni da zai jima ba a manta da radadinsa a tarihin bil’adama ba. Falasdinawa da bangaren al’ummun Israila sun tafka asarar rayuka, da dukiyoyi, da kudaden kashewa a ayyukan soji, da tabarbarewar alakar sassan kasa da kasa, da ganin baiken yaki daga sassa daban daban.
Sai dai duk da haka, sassan biyu ba su da wata mafita da ta wuce neman wanzar da zaman lafiya. Don haka sassan masu ruwa da tsaki dake da hangen nesa, ke ta maimaita batun kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, a matsayin hanya mafi dacewa ta samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Falasdinu da Isra’ila.
Yanzu dai abun zuba ido a gani shi ne ko yarjejeniyar da aka cimma za ta haifar da cikakkiyar nasarar da ake fata ko a’a. Musamman batun kafuwar kasashe biyu, da baiwa Falasdinawa cikakkiyar damar jagorancin yankinsu, da sake gina Gaza, da bude kafar biyan bukatun jin kai na al’ummar zirin da suka haura miliyan 2.1.