Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan mako wanda daga shi sai mako na gaba wato cikin Ramadan kenan, a wannan fili namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
Za mu tattauna ne akan yadda uwargida za ta gyara jikinta da Azumi, saboda Azumi kar ki ce wai yanzu Azumi ne ke ba za ki gyara jikin ki ba saboda ana Azumi ko kuma aiki ya yi miki yawa a’a ga yara shima maigida ya kamata a bashi nasa lokacin saboda ai da rana ne Azumin, bayan shan zuwa har zuwa sahur wannan ba lokaci ne na Azumi ba sannan ko Musulunci ma bai hana ma’amala ta aure ba a wannan lokacin.
- Rikicin Sudan Zai Iya Janyo Yunwa Mafi Tsanani A Duniya – WFP
- Sakataren Tsaron Amurka Ya Amince Da Samun “Kudin Yaki” A Fili
Ya kama uwargida ki zama mai iya tsarin aikin ki ta yadda zai zo miki cikin sauki da Azumi har ki samu lokacin da za ki gyara jikinki saboda maigida, ya kamata a ce ki rika shiga kicin da wuri saboda ki gama aikin ki cikin lokaci da wuri.
Za ki iya shiga kicin kamar karfe 12 na rana idan za ki yi farfesu za ki iya dora shi a wannan lokacin ki hada shi ki bar shi a wuta ya yi ta dahuwa, sannan idan kosai za ki yi za ki iya fara gyaran waken shi a wannan lokacin ki ajiye shi idan kin gama ki bar shi da ruwa ya ci gaba da jukuwa idan kuma dankali za ki yi shima za ki iya fara fere shi a wannan lokacin.
Idan kika gama fere shi ki yayyanka shi sai ki wanke ki zuba shi a colander yana shan iska kafin lokacin da za ki fara soyawa, idan kuma kin ga zai yi baki sai ki sa shi a firij kila daga nan lokaci Sallar Azahar ya yi sai ki je ki yi sallah ki dawo.
Idan za ki yi abinci sai ki dora kafin Sallar la’asar ki yi duk wani abincin da za ki yi kin gama kin sa a cooler.
Idan kunu za ki yi shima kin yi kin sa a filas ya rage miki saura suyar dankalin ko kosai ko de duk wani abin da za ki yi na suye-soye kina dawowa daga Sallal la’asar sai ki fara suyar abin da za ki yi In sha Allahu zuwa karfe 5 na yamma kin gama da kici kar ki wuce 5 da na yamma kin gyara kicin dinki kin rufe to daga nan kin gama da abinci kin kuma jera a inda ya kamata sai ki tafi zuwa wanka idan kika yi wankanki kin san ki wanke jikin ki da kika bata a kicin wani warin hayaki ne a’a abinci ya bataki duk kin gyara jikinki, sannan kafin magariba za ki iya dan yin ibadarki kafin lokacin shan ruwa.
Idan aka sha ruwa ki dan huta kafin lokacin Sallar Isha’i idan maigida ya tafi Sallar Isha kin san ana tarawi ai sai ki yi sallarki, sannan ki gyara jikinki wato ki yi wa maigida kwalliya a wannan lokacin dama kin dau wanka sai ki je ki yi duk wani shafe-shafe da za ki yi sannan kuma ga turare jikin ki ya dauka ko ina kamshi maigida zai fara jiyo kamshi tun daga kofar gida.
Sannan kuma dama kin yi turaran wuta a gidan ya zama kamar ba, a nan aka yi wannan abincin ba saboda kamshi turaran wutar duk ya kori kamshin abincin, kamshi da zai fara juyowa tun daga kofar gida na turare shi zai fara daukan hankalinsa gare ki haba koda zai shigo gida sai ya ji ashe somin tabi ne na wajen da ya fara ji ai kamshi ba’a magana.