• English
  • Business News
Saturday, May 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wane Ne Ya Shirya Rikicin Karamin Tsibirin Ren’ai Jiao?

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Wane Ne Ya Shirya Rikicin Karamin Tsibirin Ren’ai Jiao?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar ’yan sandan tsaron teku ta kasar Sin, ta fitar da wani hoton bidiyo a jiya, wanda ya nuna jirgin ruwan ’yan sanda tsaron teku na watsa ruwa a matsayin gargadi kan jiragen ruwan Philippines da suka shiga cikin yankin ruwan dake hannun riga da Ren’ai Jiao na tsibiran Nansha na kasar Sin.

Sai dai Amurka ta shafawa wannan halaltaccen hakki na tabbatar da tsaro bakin fenti.

  • Kakakin Ma’aikatar Wajen Sin Ya Yi Bayani Kan Taron Kasa Da Kasa Kan Batun Ukraine

Karamin tsibirin Ren’ai Jiao wani bangare ne na tsibiran Nansha na kasar Sin. A ranar 9 ga watan Mayun 1999, wani lalataccen jirgin ruwan yaki na rundunar sojin ruwan Philipines ya isa Ren’ai Jiao, inda aka yi ikirarin kasan jirgin na yoyo don haka aka ajiye shi a arewa maso yammacin karamin tsibirin Ren’ai Jiao kuma aka rika tura sojoji suna aikin karba-karba wajen kula da shi.

Tun daga wancan lokaci, Philippines ke ta alkawarin dauke wannan jirgin yaki, amma ta gaza cikawa. Sun kuma yi yunkurin gyara shi tare da girke karin sojoji, har ma da mamaye wannan karamin tsibiri na Ren’ai Jiao na dindindin.

A lokaci guda, Amurka ta karfafawa Philippines baya tare da taimaka mata, ta kuma tura jiragen soji da na yaki domin hada gwiwa da taimakawa a tekun.

Labarai Masu Nasaba

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

Me kake tunanin Amurka za ta yi idan jiragen ruwa na kasashen waje suka shiga yankinta na ruwa ba bisa ka’ida ba?

Wadanne irin matakai Amurka za ta dauka a kan jiragen idan suka zauna a yankinta na ruwa?

Batun na tekun kudancin kasar Sin ba shi da alaka da Amurka. Amma a shekarun baya-bayan nan, Washington na ta yada karairayi game da barazanar da ’yancin shiga tekun kudancin kasar Sin ke fuskanta, lamarin dake haifar da tankiya tsakanin kasashen yankin.

Batun na Ren’ai Jiao ya kara nuna yadda Amurka ba ta son ganin zaman lafiya a yankin tekun kudancin Sin, da kuma yadda take jiran damar tunzura al’amura a yankin. (Faeza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Sin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutane 33 A China

Next Post

Wolves Ta Dauki Sabon Koci Bayan Tashin Lopetegui

Related

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

10 minutes ago
Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

15 minutes ago
Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo
Daga Birnin Sin

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

19 hours ago
Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi
Daga Birnin Sin

Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

20 hours ago
Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani
Daga Birnin Sin

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

21 hours ago
Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha
Daga Birnin Sin

Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

21 hours ago
Next Post
Wolves Ta Dauki Sabon Koci Bayan Tashin Lopetegui

Wolves Ta Dauki Sabon Koci Bayan Tashin Lopetegui

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

May 10, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

May 10, 2025
Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu

Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu

May 10, 2025
Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

May 10, 2025
Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

May 10, 2025
Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Don Yaƙi Da Ta’addanci

Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Don Yaƙi Da Ta’addanci

May 10, 2025
Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2

Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2

May 10, 2025
Jiao

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda

May 10, 2025
Ƙungiyar Sadarwa Ta Ƙasa Ta Fitar da Sabbin Matakan Tallata Nasarorin Gwamnatin Tinubu

Ƙungiyar Sadarwa Ta Ƙasa Ta Fitar da Sabbin Matakan Tallata Nasarorin Gwamnatin Tinubu

May 10, 2025
Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi

Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi

May 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.