A yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a Kasafin Kudin shekarar 2023, al’ummar kasa da dama na sanya alamar ayar tambayar da ke neman sanin ko wane ne a cikin ‘yan takarar Shugabacin Kasa zai amfana da kasafin a wannan shekarar.
Buhari wanda ya sa hannu a Kasafin Kudin na naira tirliliyan 21. 83 tare da karamin kasafin kudin 2022 na sama da Naira biliyan 800, a ranar Talata, shi ne kasafi na karshe da ya aiwatar a matsayin Shugaban Kasa a tsayin shekaru takwas.
Manyan jam’iyyun siyasa kama daga jam’iyyar APC da ke mulkin Kasa da jam’iyyun PDP, NNPP da jam’iyyar Labour ne manyan jam’iyyun da za a yi kallon fafatawarsu a Babban Zabe da ke tafe wanda duk dan takarar da ya yi galaba a cikin su ne zai yi aiki da Kasafin Kudin na 2023 daga ranar 29 ga watan Mayu bayan saukar Shugaba Buhari.
A jawabinsa a yayin sanya a kasafin na bankwana da mulki, Buhari ya bayyana cewar an kara yawan adadin kudin ne na naira tiriliyan 21.83 da adadin naira tiriliyan 1.32 bisa ga aminta da kashe naira tiriliyan 20.51 da bangaren zartaswa ya yi tun da farko kamar yadda Mashawarcinsa na Musamman kan Yada Labarai, Femi Adesina ya bayyana a jawabin da ya sanya wa hannu a ranar Talata.
Shugaban ya ce fara amfani da kasafin kudin 2023 na da matukar muhimmanci wajen kammala ayyuka da shirin hannunta mulki cikin sauki da daukar matakan da suka kamata daga Gwamnati zuwa wata Gwamnati.
Shugaba Buhari wanda zai yi bankwana da mulki tare da hannuntawa ga wanda zai gaje shi a watanni biyar masu zuwa ya bayyana cewar dokar karin kasafin kudin 2022 za ta baiwa Gwamnatinsa damar bayar da kulawar musamman ga ambaliyar da aka fuskanta a bakidaya Kasa da samar da kan kayan more rayuwa.
Ya ce kamar yadda yake a al’adance Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmad za ta bayyana bayanai dalla- dalla na kasafin da aka aminta da shi da dokar karamin kasafin na 2022.
Wadanda suka shaidi sakawa Kasafin Kudin hannu sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila wadanda Buhari ya yaba masu tare da manbobinsu a Majalisar Kasa kan bitar kasafin da aminta da dokar kasafin kudin.
A makon jiya ne ‘yan Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai suka amince da kasafin kudin. Buhari ya bayyana cewar ‘yan Majalisar sun yi karin naira tiriliyan daya da doriya kan adadin kudin da bangaren zartawa suka tura masu domin amincewa
A cewar Buhari, sun yi nazarin canjin da aka samu daga Majalisar Wakilai a kudurin Kasafin Kudin 2023. Ya ce tsarin Kasafin Kudin da aka gyara na 2023 wanda Majalisar Tarayya ta aminta da shi ya nuna yadda aka samu karin kudin haraji na naira biliyan 765. 79 da kuma gibin da aka samu na naira biliyan 553. 46 kamar yadda ya bayyana.
Ya kara da cewar a bayyane cewar Majalisar Dokoki ta Kasa da bangaren zartaswar Gwamnati na bukatar samun karin haraji a cikin tsarin kasafin kudin wanda ya ce wajibi ne a yi gyara a kai.
Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewar ya lura yadda Majalisar Dokoki ta Kasa ta gabatar da sababbin ayyuka a cikin kasafin kudin 2023 wanda ta tsara za a kashe masu naira biliyan 770. 72. Ya ce Majalisar ta kuma kara adadin bukatun da ma’aikatu, sassa da bangarorin Gwamnati suka gabatar na naira biliyan 58. 55.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda zai zama tsohon Shugaban Kasa a ranar 29 ga watan Mayun wannan shekarar ya bayyana cewar shawarar sanya wa kasafin kudin wanda Majalisar Dokoki ta Kasa ta aminta da shi domin a fara aiwatar da aiki da shi ya faru ne musamman bisa la’akari da shirin hannunta mulki ga sabuwar Gwamnatin Dimokuradiyya.
Haka ma Shugaban ya bayar da umurni ga Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare da ta yi aiki da masu shata Dokoki domin yin bitar canjin da aka samu a kudurin kasafin kudin da bangaren zartawas suka gabatar yana mai bayyana fatan Majalisar Dokoki ta Kasa za ta ba da hadin kai ga bangaren zartaswa.
Domin ganin an fara aiwatar da ayyukan kasafin kudin na 2023, Shugaba Buhari ya bayar da umurni ga Ministar Kudi da ta fara shirin bayar da kudi cikin lokaci domin Ma’aikatu da Hukumomi su fara aiwatar da manyan ayyukansu a cikin lokaci domin su tallafawa muhimman ayyuka da inganta rayuwar al’umma.
Buhari ya sake nanata cewar an samar da kasafin kudin 2023 domin dorewar kasafin kudi, kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki, bunkasa tattalin arziki da hada kan al’umma. Ya kuma ce an yi isasshen tanadi domin gudanar da zabe tare da tabbatar da hannunta mulki ga wata Gwamnati a cikin tsanaki.
A kan wannan ya tabbatar da cewar tanadin da aka yi wa zabe mai kyau ne domin ganin an gudanar da ingantaccen zabe a cikin nasara tare da mika mulki ga Gwamnatin da za ta gaje shi.
A kan bukatar da ke akwai ta samun adadin kudin da ake bukata a kasafin kudin, Shugaban Kasa ya umurci Ma’aikatu da Bangarorin Gwamnati da Kamfunan Gwamnati da su jajirce wajen hada kan kudaden shiga ta hanyar tabbatar da dukkanin masu biyan haraji sun biya kan lokaci.
Ya ce domin tabbatar da cin moriyar muhimman ayyukan kasafin kudin 2023, wajibi ne hukumomin da lamarin ya shafa su tabbatar da dorewar samar da danyen mai da fitar da shi zuwa Kasashen waje.
Ya ce domin habaka kudaden da ake da su a kasafi, Ma’aikatu da Hukumomi za su yi hobbasar aiwatar da ayyukan hadin guiwa da bangarori masu zaman kansu musamman wadanda aka tsara domin ganin an samar da abubuwan more rayuwa cikin lokaci yana cewar a bisa ga gibin da aka samu a kasafin kudin za su mika tsarin bayar da lamuni ga Majalisar Dokoki ta Kasa ba da jimawa ba.
Baya ga wannan Shugaba Buhari ya bayyana cewar ya dogara ga hadin kan da Majalisar Dokoki ta Kasa ta bayar wajen aminta da daftarin kasafin kudin a cikin gaggawa.
A kan Dokar Kudi ta 2022 kuwa, Shugaba Buhari ya bayyana takaici kan rashin kammala nazarin dokar bayan aminta da ita da Majalisar Dokoki ta yi. Ya ce hakan ya faru ne saboda wasu sauye- sauyen da majalisa ta yi na bukatar nazari daga hukumomin da lamarin ya shafa wanda a kan hakan ya ce yana fatar za a kammala cikin hanzari domin a sa hannu ta zama doka.
Shugaban ya bayyana cewar Majalisar Dokoki mai zuwa za ta ci-gaba da gabatar da kudurin kasafin kudin shekara- shekara ga Majalisa a cikin lokaci domin ganin an zartas da shi kafin farkon shekara.
Kasafin kudin dai ya nuna an ware naira tiriliyan 6.55 domin biyan basuka, a yayin da aka ware naira tiriliyan 8.3 domin gudanar da ayyukan yau da kullum sai kuma naira biliyan 967. 48 domin amfanin hukumomi da ma’aikatu.
Fannin tsaro ya samo kaso mafi yawa na naira tiriliyan 1.1, sai biyan albashi naira biliyan 921.1, a yayin da harkokin ‘yan sanda ya samu naira biliyan 777. 4 sai fannin ilimi da kiyon lafiya da suka samu naira biliyan 663. 971 da biliyan 580. 8.
A halin da ake ciki kuma, a zantawarsa da wakilinmu na fadar shugaban kasa, Jonathan Nda-Isaiah, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan karin haske a kan kasafin kudin na bana wanda ya bayyana fatan cewa, zai saukaka wa ‘Yan Nijeriya halin da suke ciki.
“Wannan shi ne kasafin kudi na shekara ta hudu wanda kuma shi ne na karshe wanda majalisarmu ta kasa da ta wakilai ta yi aiki a kai. Kasafi ne da za a yi amfani da damar da gwamnati take da shi wajen gudanar da ayyuka na ci gab ana raya kasa. Akwai ayyuka da dama wanda kasafin nan zai taimaka kafin gwamnatin nan ta shude a gama gina gadoji, dam-dam ko matsun ruwa. Kuma muna fata wannan kasafin kudi zai kasance ya sake kawo sauki a rayuwar ‘Yan Nijeriya. Don kowa ya san halin da kasar nan take ciki.” In ji shi.